Thursday, December 2, 2021
Abubuwa guda 20 da basa karya azumi
ABUBUWAN GUDA 20 DA BA SA KARYA AZUMI1-Kwana da janaba a jiki.Annabi ya kan wayi gari da janaba kuma yana mai azumi
2-Kurkure 'baki da shaqa ruwa da yin aswaki
3-Sanya tozali da rana
@Fathul Bari
4-Sanya maganin ciwon ido
5-Sanya maganin ciwon kunne
6-Fitar maniyyi ta mafarki da rana
@Subulussalam
7-Yin qaho
@Bukhari
8-Rungumar mace da sumbatarta in ba ka da kaifin sha’awa
9-Zuba ruwa mai sanyi a fuska ko a kai
10-Dandana abinci amma a tofar bayan dandanawar
11-Amai ba da gangan ba.
12-Maganin da masu cutar ‘ASMA’ ke anfani da shi wato ( Inhaler ) lokacin azumi ba ya karya azumi
13 Shaqa maganin mura
14-Dibar jini a jikin mai azumi ba ya karya azumi
@Fatawas-siyam, Uthaymin
15-Cin abinci da mantuwa.[Allah ne ya ciyar da kai babu komi azuminka na nan]
16-Yin asuwaki ko makilin da burushi
@Siyamu Ramadana na Jamil Zainu
17-Yin wanka a rafi
18-Zuba ruwa a kai domin jin sanyi
19-Yin allura a jiki da sunan Magani bata karya azumi
20-Cire haqori ko cikesa ba ya karya azumi
@Munajjid 70 Questions on Fasting
Idan mace tana da ciki sai ta ga jini ya zubo mata a gabanta,babu komai domin wannan ba jinin haila ba ne, azuminta yana nan bai lalace ba, ciwo ne ta nemi magani.
Amma da a ce tana haila sai ta ga hailarta ta dauke bayan alfijir ya fito ba zata yi azumi ba.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Sarkakiyar Soyayya ❤️❤️❤️ Part Three
INA ASHE GUDUN BANZA NAYI HAR GIDA ZATA BIYONI TAMIN. Cikin sauri na juya da gudu nabar cikin garejin ko kayana ban chanja ba. Ina fita ko...
-
Allah has praised Enoch, describing him as being a prophet and truthful: Mention in the Book (Quran) Idris (Enoch). Verily! He was a man of...
-
llah the Almighty declared : Remember Ishmael and Idris and Dhul Kifl, all were from among those who observe patience. (Ch 21:85-86 Quran)....
-
Aysha_____ Bismillahir-rahmanir rahim إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا م...
No comments:
Post a Comment