Thursday, December 2, 2021
Banbancin Tsakanin maniyyi,maziyyi,da wadiyyi
BANBANCI TSAKANIN...* MANIYYI
* MAZIYYI
* WADIYYI
Dan Allah kudinga yin like da comment ko kuma kuyi share dinsa domin ku sami ladan wadansu su amfana.
Babu jin kunya a cikin sanin addini!
Nana A'isha tana cewa:
"Allah ya jikan MATAN MADINA kokadan KUNYA bai taba hanasu neman sanin addininsu ba"
Dan haka ga banbancin dake tsakanin su kamar haka:
(1a). MANIYYI
Maniyyin namiji: ruwane mai kauri FARI wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da zakari.
Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe yana kamshin kwai.
(1b). MANIYYIN MACE:
Ruwane TSINKAKKE, MAI FATSI-FATSI,
wani lokacin kuma yana zuwa FARI, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji.
Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, zataji tsananin sha'awa da dadi lokacin daya fito.
Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shima yana kamshin kwai.
Sannan sha'awarta zata yanke bayan fitowarsa.
HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine:
YANA WAJABTA WANKA.
(2). MAZIYYI:
Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa.
Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito.
Malamai suna cewa:
Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.
HUKUNCINSA SHINE A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA.
(3). WADIYYI
Wani ruwane mai KAURI dayake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yiba, yana fitowa ga wadanda ba suda aure, ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.
YANA DAUKAR HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI.
Ya Allah kakaramana Imani da fahimta.
Allah shine mafi sani
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Sarkakiyar Soyayya ❤️❤️❤️ Part Three
INA ASHE GUDUN BANZA NAYI HAR GIDA ZATA BIYONI TAMIN. Cikin sauri na juya da gudu nabar cikin garejin ko kayana ban chanja ba. Ina fita ko...
-
Allah has praised Enoch, describing him as being a prophet and truthful: Mention in the Book (Quran) Idris (Enoch). Verily! He was a man of...
-
llah the Almighty declared : Remember Ishmael and Idris and Dhul Kifl, all were from among those who observe patience. (Ch 21:85-86 Quran)....
-
Aysha_____ Bismillahir-rahmanir rahim إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا م...
No comments:
Post a Comment