Thursday, December 2, 2021

MATHEMATICAL MIRACLE OF QUR'AN


  MATHEMATICAL MIRACLE OF THE HOLY QUR'AN.

Da ace zaka lura, zaka ga acikin Al-qur'ani akwai wata Surah sunan ta "Suratun Nuwh", Surar annabi Nuhu, idan ka lura itace Surah ta 71, sannan zaka ga tana da ayoyi guda 28, bari mu ga wasu abubuwa guda biyar acikin wannan Surar, Suratun Nuhu itace Surah ta 71 kuma tana da ayoyi 28, Saba'in da 'daya a kwashe 28?
71-28 = 43
Zai baka 43, wannan lamba 43, shine adadin yawan sunan annabi Nuhu dake cikin Al-qur'ani gaba daya, an kira sunan "Nuhu" sau 43.
.
Abu na biyu, idan ka lura zaka ga cewa daga Suratun Nuhu zuwa 'kasa, zuwa 'karshen Al-qur'ani (Suratun Nass) zaka ga akwai surori 43 ne dai dai.
.
Abu na uku, Suratun Nuhu tana da ayoyi 28, acikin Al-qur'ani kuma Surori guda 28 ne dai dai suka ambaci sunan "Nuhu".
.
Abu na hudu, idan ka koma suratul Ankabut a ayah ta 14, zaka ga Allah yana cewa "Hakika mun tura annabi Nuhu zuwa ga mutanen sa, sai ya zauna acikin su shekaru dubu daya ba hamsin (shekaru 950) kenan.
Idan ka koma Suratun Nuhu zaka Surar tana da haruffa guda 950 dai dai idan ka cire sunan Nuhu guda daya dake farkon Surar.
.
Abu na biyar, idan kaje aya ta farko a Suratun Nuhu, zaka ayar tana da haruffa guda 49 ne:
Da farko mun ga cewa sunan annabi Nuhu yazo sau 43 acikin Al-qur'ani, toh tunda ayah ta farko tana haruffa 49, sai muce 49 a kwashe 43 zai baka saura 7.
Toh aya ta biyu a Suratun Nuhu tana da kalmomi 7.
(Daga Angon Maryama)

No comments:

Sarkakiyar Soyayya ❤️❤️❤️ Part Three

  INA ASHE GUDUN BANZA NAYI HAR GIDA ZATA BIYONI TAMIN. Cikin sauri na juya da gudu nabar cikin garejin ko kayana ban chanja ba. Ina fita ko...