▼
Thursday, December 2, 2021
YADDA MALAMI MAI YIN TAFSIR YAKAMATA YA ZAMA KAFIN YA FARA YIN TAFSIR
YADDA MALAMI MAI YIN TAFSIR YAKAMATA YA ZAMA KAFIN YA FARA YIN TAFSIR.
Da farko dai mutum barai fara yin tafsir ba sai idan ya san ya wadannan Abubuwan kafin ya fara yin tafsir
.
Reshin sanin wadannan Abubuwan shi yake kawo zagi da kage a cikin tafsirin mai yinsa
.
Abubuwan sune guda 14:
1. Ya zama Mahaddacin Al-qur'ani
.
2. Ya zama Mahaddacin wasu daga Hadisai atleast ko 2500 zuwa 3000
.
3. Ya zama yana Duba Tafsiran Malamai magabata sosai
.
4. Yasan Furu'a kuma ya karanta Furu'a saboda sanin Ahkamu wato hukunce hukencen Addini
.
5. Yasan Luggan Larabawa wato Larabci
.
6. Yasan Tasauwuf, Don samun gada a Tafsirin sa
.
7. Yasan Nahawu/lirabi
.
8. Yasan Usulul Fighu
.
9. Yasan Usulul Dinu
.
10. Yasan fannin Balaga
.
11. Yasan Asbabun Nuzul
.
12. Yasan Nasikh da Mansukh
.
13. Yasan Tarihin Addinin Musulunci wato "Siyar
.
14. Yasan Ilmul Qiraa'aat
.
Ko da shike IMAMU ASSUYUDI yace Abubuwan sun kai Almost 50 to 55
.
Amma wadannan 14 sune Manyan a lamarin Addini
.
To in mutum bai san su ba bai kamata ya ajiye littafi a gabansa wai da sunan yana tafsir ba
No comments:
Post a Comment